
Shugaban Kamfanin BUA, Abdul Samad Rabiu, ya ce kamfanin ya amince da karin albashin ma’aikatan shi kashi hamsin cikin dari.
Rabiu ya bayyana hakan ne a cikin wata takarda ta cikin gida da Mohammed Wali, shugaban ma’aikata na BUA ya sanya wa hannu a ranar Lahadi a Legas.
Sanarwar ta ruwaito cewa shugaban BUA na cewa anyi karin kudin albashin ne domin rage tasirin matsalolin tattalin arzikin da kasar nan ke fuskanta a halin yanzu.
Ya ce karin albashin ya shafi ma’aikata na dindindin, na yau da kullum da wadanda ba na dindindin ba daga ranar daya ga watan nan.
Ya ce, Bayan wannan ci gaban da aka samu, sashen hada-hadar kudi na kamfanin suna kan aiki domin aiwatar da karin don tabbatar da cewa an zura karin albashin a cikin albashin da za a biya cikin wannan watan da muke ciki.
Ya ce, “Muna fatan da wannan gagarumin karimcin, za mu kara himma wajen gudanar da ayyukan mu tare da yin iya kokarin mu don tabbatar da kwarin gwiwar da aka yi mana.”
Ana ci gaba da tattaunawa tsakanin kungiyoyin kwadago da gwamnati, kan sabon mafi karancin albashi sakamakon yanayin tattalin arzikin da kasar nan fama da shi.