Back

Yanzu-yanzu: Kungiyoyin Kodago sun sanar da fara yajin aiki nan da kwanaki 14 kan matsalolin rayuwa

Kungiyar kwadago ta Najeriya da takwararta ta ‘yan kasuwa sun fitar da sanarwar fara yajin aiki nan da kwanaki goma sha hudu a duk fadin kasar, idan gwanatin Bola Ttinubu Bata dauki matakai na magance matsalolin rayuwa da ke addabar ‘yan Najeriya ba.

Kungiyoyin din nuna rashin Jin dadi da amincewa kan gazawar gwamnatin Tinubu wajen aiwatar da yarjejeniyoyin da aka cimma a ranar biyu ga watan goma na shekarar bara.

Hakan ya biyo bayan kawar da tallafin man fetur wanda gwamnatin tarayyar ta yi a lokacin rantsar da shugaban kasar a shekarar da ta gabata.

Shugabannin kodagon na NLC da TUC sun nuna bakin cikin cewa duk da kokarin da kungiyoyin kwadago ke yi na tabbatar da zaman lafiya a masana’antu, da alama gwamnati ba ta damu da dimbin wahalhalun da jama’a ke fama da su ba a fadin kasar nan.

Yarjejeniyar ta ranar biyu ga watan goma “ta mai da hankali ne kan magance dimbin radadin da ake fama da shi da kuma illatuwa da tattalin arzikin kasa ya samu inda suka nuna cewa akwai rashin lissafi da rashin yin garanbawul kan al’amuran yau da kullum na kasar ciki har da faduwar darajar Naira.

“Wadannan tsare-tsare na gwamnati,, kamar yadda muka yi hasashe, sun haifar da mummunar illa ga tattalin arziki da talakawa da ma’aikatan Najeriya,” in ji sanarwar da kungiyoyin suka fitar a yau Alhamis.

Da suke karin haske, akan matsalolin, kungiyoyin sun koka da cewa “abin takaici ne yadda aka tilasta mana daukar irin wadannan matakai, amma rashin kula da jin dadin ‘yan kasa da ma’aikatan Najeriya da kuma tsananin wahalhalu ya sa ba mu da zabi sai dai aiwayarwa.”

Daga ranar tara ga wannan watan na Fabreru (gobe Jumma’a) sauran kungiyoyin kwadagon biyu suka bayyana cewa za su dauki kwanaki goma Sha hudu kafin su fara yajin aikin idan Gwamnatin bata gyara ba.

Kungiyoyin din ce saboda sanin gaggawar lamarin, da kuma wajibcin tabbatar da kariya da kare hakki da mutuncin ma’aikata da ‘yan Najeriya, NLC da TUC suka baiwa Gwamnatin Tarayya wa’adi mai tsauri da ta aiwatar da su cikin kwanaki 14 daga gobe Tara ga watan Fabrairu, 2024.”

Daga cikin abubuwan da gwamnatin tarayya ta yi alkawarin aiwatara bata cika ba har da shirin biyan albashin ma’aikata N35,000 wanda har yanzu ba a fara biya ba.

Wakilin Mu
Wakilin Mu
https://www.btvhausa.com

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?