
Likitocin kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles ta wanke dan wasa, Victor Osimhen domin garzayawa karawar kusa da karshe da Afrika ta Kudu.
Za a iya tunawa, Dan wasa Victor Osimhen bai samu zuwa buga wasan kungiyar kwallon kafar ta Super Eagles da za su yi a Karo na kusa da karshe da kasar Afirka ta kudu ba a Bouake biyo bayan fama da ciwon ciki da yayi.
An ce za a duba dan wasan na Napoli a safiyar yau Talata, kuma idan likitocin suka wanke shi, zai shiga cikin sauran ‘yan wasan da suka isa Bouake lafiya.
A yanzu haka, a cewar majiyoyi daga kasar Abidjan, Osimhen na kan hanyar sa ta zuwa Bouake ne bayan da tawagar likitocin ta bayyana cewar ya samu lafiyar sa zai iya buga wasan.
Dan wasan mai shekaru 25 ya fara buga wasanni biyar na Super Eagles a Cote d’Ivoire, inda ya zura kwallo daya.