
Murja Kunya
Shahararriyar ‘yar TikTok ta Kano, Murja Ibrahim Kunya, ta nemi beli daga Babbar Kotun Tarayya da ke Kano.
Wata babbar kotun shariah ta tsare ta kuma ta ba da umarnin a duba lafiyar ƙwaƙwalwar ta.
Mai Shari’a Nasiru Saminu ya ƙi amincewa da buƙatar neman belin ta a wata ƙara da ya gudanar.
Sai dai lauyan Kunya, Barista Yusuf Ali Faragai, ya nemi a bayar da belin ta a Babban Kotun Tarayya, yana mai cewa laifin da ake zargin yana da beli.
Lauyan ya buƙaci da ya san inda take daga waɗanda ake tuhumar domin a tantance lafiyarta, inda ya buƙaci masu gabatar da ƙara su gabatar da ita a gaban kotu.
Waɗanda ake ƙara a cikin ƙarar sun haɗa da Babban Lauyan Kano, Hukumar Hisbah ta Kano da Kotun Shari’a ta Jihar Kano, Kwana Hudu.
Sai dai Lauyan waɗanda ake ƙara, Barista H.H Suleiman, ya nuna rashin amincewa da buƙatar.
Ya ƙara da cewa ƙarar cin zarafi ne na tsarin kotu bayan ya shigar da irin ƙarar a gaban wata babbar kotun jihar.
Mai shari’a Abdullahi M Liman ya ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 28 ga Maris, 2024 domin yanke hukunci.