Back

Yara suna mutuwa saboda yunwa a asibitocin arewacin Gaza, inji WHO

Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta bayyana cewa wata tawagar agaji da ta ziyarci asibitoci biyu a arewacin Zirin Gaza ta gano yadda ɗimbin yaran Falasɗinawa ke mutuwa saboda yunwa, a cikin matsanancin ƙarancin abinci, man fetur, da magunguna.

Abubuwan da aka gano sun kasance “munana”, a cewar shugaban WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus a kafar X, ya kuma ƙara da cewa, “Halin da ake ciki a Al Awda ya kasance mai ban-tsoro saboda ɗaya daga cikin gine-ginen ya rushe”.

Asibitin Kamal Adwan, wanda shi ne kaɗai asibitin kula da yara a arewacin Gaza, ya cika da majinyata, inji shi.

“Rashin abinci ya yi sanadiyyar mutuwar yara goma,” inji Tedros.

A halin da ake ciki, ƙungiyar da ke birnin Geneva, Euro-Med Human Rights Monitor, ta bayyana wata shaida mai tayar da hankali a cikin wata sanarwa da ta fitar da ke nuna cewa tankunan yaƙi na Isra’ila sun bi ta kan Falasɗinawa da gangan a ranar Lahadi.

Ƙungiyar, wadda ke da hedikwatar ta a birnin Geneva, ta bayyana waɗannan laifuka a ranar Litinin a matsayin “wani ɓangare na kisan gillar da Isra’ila ke yi wa Falasɗinawa a Zirin Gaza.”

Euro-Med ta ba da rahoton ƙararraki na sojojin Isra’ila da suke bi ta kan Falasɗinawa a raye, ciki har da wani mutum a ranar 29 ga Fabrairu, iyali a ranar 23 ga Janairu, mutanen da suka yi gudun hijira a Disamba 2023, da wasu iyalai a ranar 20 ga Fabrairu.

Har ila yau, ta yi kira ga “Kwamitin bincike na ƙasa da ƙasa mai zaman kan sa wanda ya gudanar da bincike kan harin soji da Isra’ila ke kai wa Zirin Gaza.”

Isra’ila ta ƙaddamar da wani farmaki a Zirin Gaza bayan kutsawar da dakarun ƙungiyar Hamas suka yi a kan iyakokin ƙasar a ranar 7 ga Oktoba, 2023.

Yayin da harin bam da Isra’ila ke kai wa ya shiga kwana na 150, Isra’ila ta kashe aƙalla Falasɗinawa 30,534, galibi yara da mata, tare da raunata wasu 71,980 da kuma ɓarnatawa da jawo ƙarancin kayan masarufi.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?