Back

Yarima Harry ya ziyarci Kaduna domin ganin sojojin da suka samu raunuka

Yarima Harry da Gwamna Uba Sani

Duke na Sussex, kuma ɗa na biyu ga Sarki Charles na Burtaniya, Yarima Harry a ranar Juma’a ya kai ziyara Jihar Kaduna a wani ɓangare na ziyararsa zuwa Nijeriya.

Da yake magana a lokacin da Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, da wasu jami’an gwamnati suka tarbe shi a gidan Sir Kashim Ibrahim, Kaduna, Yarima Harry ya ce abin da ya fi mayar da hankali a kai shi ne ganin sojojin da suka samu raunuka a lokacin da suke yi wa ƙasa hidima, da kuma iyalan waɗanda aka kashe a fagen daga.

Ya ce bayan kafa wata ƙungiyar agaji da ke kula da jin daɗin sojoji shekaru 10 da suka gabata, Nijeriya ita ce ƙasa ta farko a Afirka da ta fara cin gajiyar wannan ƙungiyar tare da sojoji 10 da za su ci gajiyar wannan tallafin.

“Mun tattauna da Babban Hafsan Hafsoshin Tsaron Nijeriya ‘yan sa’o’i kaɗan da suka gabata kuma zuwanmu Nijeriya ya sanya murmushi a fuskokin sojojin da suka samu raunuka,” inji shi.

Gwamna Sani, a lokacin da ya karɓi baƙuncin iyalan gidan sarautar Burtaniya a gidan Sir Kashim Ibrahim, ya ce Yarima Harry abin zaburarwa ne ga matasa kuma abin koyi ne na kishin ƙasa.

“Na yi matuƙar farin cikin maraba da Yarima Harry, Duke na Sussex, zuwa Jihar Kaduna, bugun zuciyar Arewacin Nijeriya da Cibiyar Ilmantarwa ta Nijeriya. Ziyarar ku ta tuna mana da wani abin farin ciki shekaru 68 da suka gabata, lokacin da mai girma jagoranmu, Firimiyan Arewacin Nijeriya, Sir Ahmadu Bello ya yi wa Sarauniya Elizabeth ta biyu, kakarku, maraba a Kaduna a ranar 2 ga Fabrairu, 1956.”

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?