Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kaduna (KSPWA) ta tunatar da dukkan maniyyatan da ke da niyyar zuwa aikin hajjin bana, cewa wannan Litinin ɗin ce ranar ƙarshe ta yin rajistar maniyyata aikin hajjin shekarar 2024.
Hakan ya biyo bayan tsawaita wa’adin da Hukumar Alhazai ta Najeriya (NAHCON) ta sanar a makon da ya gabata.
Yunusa Mohammed Abdullahi, Mai Magana da Yawun Hukumar KSPWA, ya jaddada cewa zuwa yau ne waɗanda suka yi rajista kuma suka kammala biyan kuɗin aikin Hajji kawai za su iya sauke farali daga jihar Kaduna.
Ya kuma buƙaci dukkan maniyyatan da ba su kammala rajista ko biya ba da su gaggauta yin hakan.
Sanarwar ta ce “KSPWA ta himmatu wajen tabbatar da samun nasarar aikin Hajji ga dukkan maniyyata,” in ji shi, ya kuma ƙara da cewa, ”Sannan kuma ana maraba da sabbin masu shiga da su yi rajista a yau, idan har an samu kujerar Hajji.”
A cewarsa, sama da mutane 4,000 ne suka bayyana sha’awarsu ta zuwa aikin Hajji daga Kaduna, kuma Hukumar KSPWA ta duƙufa wajen taimaka wa duk wanda ya cancanta.
Hukumar NAHCON ta ware kujeru 6,004 ga jihar Kaduna daga cikin sama da 95,000 da ake sa ran za su yi aikin Hajji daga Najeriya a bana.
Tare da ƙarancin kujeru, KSPWA ta buƙaci duk masu sha’awa su yi rajista zuwa wa’adin ƙarshe don guje wa ɓacin rai.