Back

Za a fara biyan sabon mafi ƙarancin albashi daga 1 ga Mayu, 2024, inji Gwamnatin Tarayya

Daga Hagu: Ministar Ƙwadago, Nkiruka Onyejeocha, Shugaban NLC, Joe Ajaero, Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima, da Shugaban TUC, Festus Osifo, a Abuja ranar 1 ga Mayu, 2024

Gwamnatin Tarayya ta ce duk da cewa kwamitin da ke kula da mafi ƙarancin albashi na ƙasa bai kammala tattaunawarsa ba, za a fara biyan sabon mafi ƙarancin albashin ma’aikata daga 1 ga Mayu, 2024.

Ƙaramar Ministar Ƙwadago, Nkeiruka Onyejeocha ne ta bayyana hakan a ranar Laraba yayin da take jawabi ga ma’aikatan Nijeriya a wajen bikin Ranar Mayu a Abuja.

Ta ce abin takaici ne yadda ba a shirya sabon mafi ƙarancin albashi na ƙasa kafin yau ba, amma ana ci gaba da shawara domin ganin an fitar da takardar da wuri.

Ƙungiyoyin ƙwadagon Nijeriya na NLC da TUC a lokuta daban-daban sun yi kira ga gwamnatin Shugaban Ƙasa Bola Tinubu da ta gaggauta ƙara albashin ma’aikata.

Daga baya ƙungiyar ƙwadago ta buƙaci naira 615,000 a matsayin sabon mafi ƙarancin albashin ma’aikata domin shawo kan ɗimbin matsalolin tattalin arziƙi da tsadar rayuwa a Nijeriya.

Ƙungiyoyin ƙwadagon sun ce mafi ƙarancin albashi na naira 30,000 a halin yanzu ba zai iya samar da jin daɗin ma’aikatan Nijeriya ba, suna masu ƙorafin cewa ba dukkan gwamnoni ne ke biyan albashin ma’aikata na yanzu ba wanda ya ƙare a watan Afrilu, shekaru biyar bayan Dokar Mafi Ƙarancin Albashi na 2019 da Tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya sanya wa hannu. Za a sake duba dokar duk bayan shekaru biyar don biyan buƙatun ma’aikata na tattalin arziƙi na zamani.

A halin da ake ciki, Shugaba Tinubu ya yaba da gudunmawar da ma’aikata ke bayarwa a Nijeriya wajen ci gaban ƙasar.

Ya yi wannan yabon ne a jawabinsa ga ma’aikatan da Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ya gabatar a wajen taron bikin ranar ma’aikata ta 2024 a Abuja.

Ya ce Gwamnatin Tarayya a shirye take da ta karɓi shawarwarin kwamitin kan sabon mafi ƙarancin albashi na ƙasa.

Ya ba da tabbacin cewa shirin kawo sauyi na gwamnatin da ke ci a yanzu ya karkata ne ga ci gaban Nijeriya.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?