Back

Za a fara samar da wutar lantarki mai dorewa a Aba a karshen wannan makon

Kamfanin wutar lantarki na Aba Power Ltd, na kamfanin Geometric Power, zai fara samar da wuta daga daya daga cikin injina guda uku da suke girke ga masu amfani da wutar a yankin Aba ring-fence area a karshen makon nan, makonni biyu gabanin ranar da aka tsara za su fara aikin tun farko.

Kamfanin ya tsara samar da kayayyaki ga masu amfani da wutar, da  ‘yan kasuwa, kwanaki goma sha uku bayan kaddamar da aikin, amma kamar yadda majiyoyi suka bayyana, shugaban kamfanin, Farfesa Bart Nnaji, wanda tsohon ministan wutar lantarki ne, ya umurci injiniyoyin kamfanin da su samar da wutar lantarki ga jama’a a karshen mako nan.”

Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, a madadin shugaba Bola Tinubu, ya kaddamar da kamfanin samar da wutar lantarki na Geometric Power mai 188 Megawatt da kuma kamfanin Aba Power wanda zai raba wutar lantarkin ga kananan hukumomi tara daga cikin goma sha bakwai na jihar Abia a ranar Litinin din da ta gabata.

An ba wa Jami’an Hukumar Kula da Makarantu na Kasa (NCC) a Oshogbo a Jihar Osun takardar izinin duba cibiyar samar da wutar lantarkin.

Yayin da daya daga cikin na’urorin injina uku da aka gina na Geometric Power da General Electric na kasar Amurka ya fara kasuwanci a karshen makon nan, zai samar da megawatt 47, wanda kusan ya ninka megawatt 25 da cikin garin Aba da kewaye ke samu daga kamfanin Neja Delta Power Holding Company (NDPHC).

Injin mai na biyu, zai kara samar da wutar lantarki a wasu yankunan na Aba zuwa megawatt 94, ta yadda za a samarwa da al’ummar biyan bukatun su a Aba a halin yanzu da kuma daidaita wutar lantarki a yankin.

Najeriya na bukatar kamfanoni masu kere-kere da masu rarraba kayan aikin wuta na zamani kamar Geometric Power, wanda kamfanin hadaddiyar kungiyar wutar lantarki ce, tana da rassan da ke samarwa da rarrabawa.

Kamfanin Neimeth Pharmaceuticals Plc da ke Legas na daya daga cikin manyan kamfanonin da suka bayyana aniyar mayar da masana’antun su zuwa Aba a lokacin da wutar lantarki ta inganta sosai a yankin masana’antu.

Ministan Wutar Lantarki, Adebayo Adelabu ya bayyana a wajen kaddamar da cibiyoyin samar da wutar lantarki cewa gwamnatin tarayya za ta yi nazari sosai a kan yadda kungiyar samar da wutar lantarki ta Geometric za ta yi aiki da ita da nufin ganin ta zama abin koyi ga ci gaban bangaren wutar lantarkin Najeriya da ke fama da matsaloli.

Wakilin Mu
Wakilin Mu
https://www.btvhausa.com

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?