Back

Za a gudanar da taron kwamitin harkar kudade na babban bankin Najeriya karo na 293 da sabbin fuskoki a ranar Litinin, Talata

Babban Bankin Najeriya (CBN) ya sanar da taron kwamitin kula da harkokin kudi na kasa (MPC) karo na dari biyu da casa’in da uku da ake sa ran za a yi a ranakun ishirin da shida da ishirin da bakwai ga watan nan. 

Wannan taro mai mahimmanci zai yi tasiri mutuka wajen kawo ci gaba tare da sabbin ƙwararrun masana hada-hadar kuɗi waɗanda ke da burin tsara yanayin tattalin arziki.

Taron zai gudana ne a dakin yaron kwamitin da ke hawa na sha daya na hedikwatar babban bankin da ke Abuja da karfe goma na safe ranar Litinin kuma da karfe takwas na safiyar Talata.

Za a saka dukkanin idanuwa kan sabbin mambobin kwamitin da aka tabbatar, wadanda za su hau kujerun su a karon farko.

Wannan rukunin daban-daban ya ƙunshi fitattun mutane kamar Dokta Aloysius Uche Ordu; kwararre kan harkokin kudi Lamido Abubakar Yuguda da fitattun malamai kamar Dr. Mustapha Akinkunmi da Farfesa Murtala Sabo Sagagi.

Za su shiga cikin mambobin da ake da su, har da Gwamna, mataimakan gwamnoni hudu da babban sakatare na ma’aikatar kudi. Wadannan sun kasanve kwararru kan hakkokin Kuɗaɗen dalilin da yasa suka zama wata babbar tawaga mai dimbin kwarewa.

Wannan taro yana da matukar muhimmanci yayin da ya kasance a wani muhimmin lokaci na tattalin arziki.

Har yanzu hauhawar farashin kayayyaki ya kasance babban abin damuwa yayin da rashin tabbas kan tattalin arzikin duniya ke ci gaba da yin barna.

Hukunce-hukuncen da kwamitin ta yanke kan kudaden ruwa, yawan ruwa, da sauran ka’idojin tsare-tsare na kudi za su yi tasiri kai tsaye kan jakunkunan ‘yan Najeriya da kuma lafiyar tsarin hada-hadar kudi.

Tabbacin da majalisar dattawa ta yi kwanan nan kan sabbin mambobin kwamitin, ciki har da Gwamna Olayemi Cardoso a matsayin shugaba na nuna muhimmancin da aka ba wa wannan taro da kuma yadda zai iya yin tasiri a kan turbar tattalin arzikin kasa.

Wakilin Mu
Wakilin Mu
https://www.btvhausa.com

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?