Shugaban Ƙasa, Bola Tinubu, ya yi Allah-wadai da kashe jami’an soji a jihar Delta, yana mai cewa waɗanda suka aikata wannan aika-aika, waɗanda ya bayyana a matsayin matsorata, ba za su tafi ba tare da an hukunta su ba.
An kashe jami’an soji da suka haɗa da kwamanda ɗaya da wasu Manjo biyu da Kyaftin ɗaya da sojoji goma sha biyu tare da farar hula ɗaya a cikin al’ummar Okuama da ke ƙaramar hukumar Ughelli ta Kudu a jihar Delta a makon jiya yayin wani aikin ceto.
Amma da yake mayar da martani kan lamarin, Tinubu a cikin wani saƙo da ya fitar a yammacin Lahadi, ya ce kisan “wanda ba a takala ba ne” kuma “mummuna ne”.
“A matsayina na Babban Kwamandan Rundunar, ina haɗa kai da dukkan ‘yan Nijeriya masu kishin ƙasa da maza da mata na sojojin mu don yin alhini tare da nuna baƙin cikina game da mutuwar manyan sojojin mu,” inji Tinubu.
“Ina miƙa ta’aziyyata ga iyalan waɗannan sojoji da suka mutu, abokan aikinsu, da kuma ‘yan uwansu. Tuni dai babban hafsan sojin ƙasar ke mayar da martani kan wannan lamarin. Sai matsoratan da suka aikata wannan ɗanyen aikin sun fuskanci hukunci.”
A cewarsa, kisan na ƙara nuna irin hatsarin da maza da mata ke fuskanta a bakin aikinsu.
“Ina jinjinawa jarumtakarsu, jajircewa, da kuma kishin ƙasa,” inji shi.
“A matsayinmu na al’umma, dole ne mu ci gaba da tunawa da kuma girmama duk waɗanda suka rasa rayukan su don tsaro, ƙarfi da kuma haɗin kan ƙasar mu. Hafsoshin da mazan da suka mutu a yankin Okuama sun bi sahun manyan maza da mata waɗanda suka sadaukar da komai, a hidimar ƙasar mu.
“Sojojin mu su ne jigon ƙasarmu. Duk wani hari da aka kai musu hari ne kai tsaye ga al’ummarmu. Ba za mu yarda da wannan mugun aiki ba.”
Tinubu ya ce an baiwa hedikwatar tsaro da Hafsan Hafsoshin Tsaron Ƙasar cikakken ikon gurfanar da duk wanda aka samu da hannu wajen aikata wannan aika-aika da ake yi wa al’ummar Nijeriya.
“Gwamnatina ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba har sai mun samu zaman lafiya da kwanciyar hankali a kowane ɓangare na Nijeriya,” inji shi.