Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya jaddada aniyar gwamnatin sa na kawo ƙarshen ‘yan bindiga a Jihar Zamfara.
Shugaban Ƙasar ya ba da umarnin tura sojoji tare da ci gaba da kai farmaki kan ‘yan bindiga a Zamfara.
Wata sanarwa da mai magana da yawun Gwamnan Zamfara, Sulaiman Bala Idris, ya fitar ta ce, Shugaban Ƙasa Tinubu ya tarbi wasu gwamnonin jihohi da shugabannin Majalisar Dokoki a gidansa da ke Legas.
A cewar sanarwar, tawagar ƙarƙashin jagorancin mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ta kai wa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu gaisuwar Sallah a ranar Juma’a.
“A yayin tattaunawa da Gwamna Dauda Lawal, Tinubu ya yi tambaya game da matsalar tsaro a jihar Zamfara.
“Gwamna Lawal ya sanar da Shugaban Ƙasar irin ci gaban da aka samu da kuma yadda sojoji ke ci gaba da yaƙi da ‘yan bindiga a jihar.
“Shugaban Ƙasa Tinubu ya tabbatar wa gwamnan cewa ya ƙuduri aniyar kawo ƙarshen matsalar ‘yan bindiga a jihar, inda ya ƙara da cewa ya bayar da umarnin ci gaba da kai farmakin sojoji tare da tura ƙarin sojoji Jihar Zamfara.
“Ya buƙaci ƙarin bayani akai-akai daga Gwamna Lawal game da yanayin tsaro na jihar don ingantaccen haɗin gwiwa a yaƙi da ‘yan bindiga.”