
Batutuwa a fannin wutar lantarki na da bangarori da dama, masu sarkakiya, in ji minista
• Gwamnatin Tarayya ta zuba makudan kudade a bangaren makamashi – inji Adelabu
Ministan wutar lantarki, Adebayo Adelabu, ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa matsalolin da suka dabaibaye bangaren wutar lantarkin kasar nan ba da dadewa ba za su zama abin tarihi.
Ya kuma bayyana cewa gwamnatin tarayya ta zuba makudan kudade a fannin makamashi, amma ya ce abin takaici ne yadda akasarin ‘yan Najeriya ke fama da kalubalen wutar lantarki.
Adelabu ya bayyana haka ne a ziyarar da ya kai kamfanin samar da wutar lantarki ta Ihovbo da ke karamar hukumar Uhunmwonde a jihar Edo.
Ya ce: “Na zagaya kayan aikin, kuma na ga abin da muke da shi ya burge ni sosai. Sabanin yadda kowa ya sani, Najeriya ta zuba jari sosai a masana’antar samar da wutar lantarki. Ga kayan aiki na zamani, kuma ana kiyaye su da kyau. Ga wurin da hada su yanayi ne da ya dace wanda zai iya ba mu nau’in samar da wutar lantarki da muke bukata a kasar nan, sai dai ana yin aiki maras fasali.
“Na isa gidan wutar lantarki na Ihovbo, wanda mallakar gwamnatin tarayya ne, a karkashin kamfanin Neja Delta Power Holding Company. Ita ce zango mai iskar gas guda hudu, tana wurin da ya dace, mai karfin megawatts kusan dari da ashirin da biyar kowacce, adadin ya kai megawatts dari biyar.
Adelabu yace, kayan wutar suna girke a wurin da ya dace, inda kuma ake kula da su sosai, amma ba a yi amfani da su yadda ya kamata ba, hakazalika ba a yi aiki da su sama da shekaru uku ba duk da cewa an girka su a wurin tun kusan shekaru takwas ko goma da suka gabata.
“Sabbin injina ne, amma abin mamaki, injin guda daya ne kawai ke aiki a halin yanzu, wanda ke samar da wutar lantarki kusan megawatts dari, sabanin yadda aka girka na megawatts dari biyar, wanda kashi ashirn ne kawai ake amfana da su, kuma hakan ke zama babban dalilin rashin inganta wutar lantarki, hakan ke dakile burin mu na amfana da wutar a matsayin babban jarin mu na kasa.”
“Idan har mun saka himma sosai wajen kafa cibiyoyin samar da wutar lantarki, ya kamata ta iya ba mu irin wutar da muke bukata. Abin da ke haifar da tashin hankali shine karancin iskar gas, wanda a yanzu muke kokarin samarwa. Labari mai dadi shine, taimakon yana kusa da mu, agaji yana kusa da wadannan cibiyoyin samar da wutar lantarkin, kamar yadda Gwamnatin Tarayya, tare da Ma’aikatar Kudi ta Tarayya, Ma’aikatar Kasafin Kudi da Tsare Tsaren Tattalin Arziki ta Tarayya, da Ma’aikatar Wutar Lantarki ta Tarayya suka gana da Shugaba Bola Tinubu, kuma ya umarce mu da mu je mu tsara yadda za mu yi karbo basusukan da ake bi.”
Ministan wutar lantarkin ya kuma bayar da tabbacin cewa nan ba da dadewa ba ’yan Najeriya za su ci gajiyar wutar lantarki ba tare da katsewa ba da sauran ribar dimokuradiyya.
Ministan ya bukace ‘yan Najeriyan da su ci gaba da marawa gwamnatin Tinubu wadda ta mayar da hankali domin ciyar da al’ummar kasar gaba sosai.