Shugaban Amurka Joe Biden ya yi gargaɗi ranar Juma’a cewa zai yi matuƙar wahala a samar da tsagaita wuta tsakanin Isra’ila da Hamas a watan Ramadan mai alfarma.
“Yana da wahala,” Biden ya faɗawa manema labarai lokacin da aka tambaye shi ko za a iya cimma yarjejeniyar dakatar da rikicin da aka shafe watanni biyar ana yi a watan Ramadan, wanda zai fara ranar Lahadi idan an ga wata.
Biden ya ƙara da cewa na damu matuƙa game da yiwuwar tashin hankali a gabashin Ƙudus da Isra’ila ta mamaye yayin da watan Ramadan ke gabatowa, yana mai ƙara irin wannan gargaɗin da ya yi a farkon wannan makon.
Ƙungiyar Hamas da ke ɗauke da makamai a ranar Juma’a ta buƙaci magoya bayanta da su yi gangami zuwa harabar masallacin Al-Aqsa da ke gabashin birnin Ƙudus, wani wurin tashin hankali a cikin watan Ramadan a shekarun da suka gabata.
Har ila yau, ta ce ba za a yi sulhu ba kan buƙatar ƙungiyar ta Isra’ila ta janye daga Gaza domin ganin an sako mutanen da Hamas ta yi garkuwa da su.
Yaƙin Isra’ila da Hamas dai ya samo asali ne sakamakon harin da ‘yan gwagwarmayar Falasdinawa suka kai a kudancin Isra’ila a ranar 7 ga watan Oktoban 2023.