Back

Zaki ya kashe ma’aikacin jami’ar Najeriya a harabar jami’a

Wani likitan dabbobi da ke aiki a Jami’ar Obafemi Awolowo (OAU), Ile-Ife, Olabode Olawuyi, a ranar Litinin ɗin da ta gabata wani zaki ya kai masa hari tare da kashe shi a gonar dabbobin makarantar.

Wannan labarin na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da jami’ar ta fitar a ranar Litinin mai ɗauke da sa hannun Jami’in Hulɗa da Jama’a na na ta, Abiodun Olarewaju.

Olarewaju, wanda ya bayyana shekarun zakin tara, ya ce marigayin ya kasance yana kula da shi tun lokacin da aka haife shi a jami’ar.

Ya ce dabbar ta kekketa Olawuyi a lokacin da yake ciyar da su a lambun dabbobin, kuma ƙoƙarin da sauran ma’aikata suka yi na ceto marigayin ya ci tura.

Sai dai sanarwar ta ƙara da cewa a ƙarshe an kashe zakin cikin halin mutuntaka bayan rasuwar jami’in.

Sanarwar ta ƙara da cewa: “An jefa masu gudanarwa, ma’aikata, ɗalibai, da ɗaukacin jami’ar Obafemi Awolowo, Ile-Ife, jihar Osun, cikin alhini sakamakon rasuwar Olabode Olawuyi.

A cewar sanarwar, mataimakin shugaban jami’ar, Adebayo Bamire ne ya jagoranci ma’aikatan zuwa wurin da lamarin ya faru domin tantance halin da ake ciki.

Olarewaju ya ce, a lokacin da mataimakin shugaban jami’ar da tawagar shi suka ziyartarci, wurin da lamarin ya faru, sun samu bayanan kokarin da muƙaddashin daraktan cibiyar lafiya da na magani na makarantar, Tirimisiyu Olatunji ya yi na ceto marigayin amma ba a samu nasara ba.

Sanarwar ta ci gaba da cewa: “Sauran ma’aikatan da ke wurin da lamarin ya faru sun yi duk abin da za su iya yi domin ganin sun ceto ubangidan nasu amma zakin ya riga ya yi sanadin salwantar rai.

“Da jin wannan labari mai ban tausayi, masu gudanarwa ƙarkashin jagorancin mataimakin shugaban jami’ar, ba zato ba tsammani suka kawo ƙarshen wani taro da ke gudana domin tantancewar nan take. 

Ya ce tuni jami’ar ta aike da wakilai zuwa ga matar marigayin da ‘ya’yan shi, inda ta roƙe su da su yi ta’aziyya ga Allah wanda yake rayawa kuma yana da ikon ɗaukar rai.

A halin da ake ciki, jami’ar ta ce mataimakin shugaban jami’ar ya ba da umarnin “cikakken bincike kan musabbabin faruwar lamarin.”

Wakilin Mu
Wakilin Mu
https://www.btvhausa.com

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?