Back

Zamu tabbatar da kariyar bayanai daga kamfanoni masu amfani da AI, inji NCC

Hukumar Sadarwa ta Nijeriya (NCC) ta ce tana aiki da hukumomin da abin ya shafa don tabbatar da cewa kamfanoni sun tabbatar da kare bayanan ‘yan Nijeriya yayin amfani da na’ura mai ƙwaƙwalwa wacce ke kwaikwayon ɗabi’un mutane (AI).

Mataimakin shugaban hukumar ta NCC, Aminu Maida, ne ya bayyana hakan a ƙarshen mako a Abuja yayin bikin Ranar Kare Haƙƙin Masu Amfani ta Duniya na shekarar 2024, mai taken “Fair and Responsible Al for Consumers.”

Maida, wanda ya samu wakilcin Abraham Oshadami, Kwamishinan Zartarwa, Ayyukan Fasaha, ya ce AI tuni ta fara yin sabbin abubuwa a fannin kiwon lafiya, kuɗi, sufuri, da dai sauransu.

Duk da haka, ya lura cewa duk da cewa waɗannan sabbin abubuwa suna da kyau, yin amfani da AI yadda ya dace yana da muhimmanci don tabbatar da amincin masu amfani da keɓance matsaloli masu yuwuwa.

Ya ce, “AI Da Ya Dace yana nufin amfani da shi ta hanyar ɗa ya dace a duk lokacin ƙirƙirar sa, turawa da kuma amfani da shi.

“Wannan ya haɗa da la’akari da batutuwa kamar son zuciya, sirri, bayyana gaskiya da riƙon amana. A cewar rahotanni, AI Da Ya Dace yana da niyyar ƙarfafa masu amfani, gina amana da rage mummunan tasiri.”

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?