Back

Zan yarda da haɗewar jam’iyyar Labour da PDP idan zai inganta Nijeriya – Peter Obi

Ɗan takarar Shugaban Ƙasa na jam’iyyar Labour a shekarar 2023, Peter Obi, ya ce yana da burin ganin Nijeriya ta inganta amma ba ya fatan zama Shugaban Ƙasa ido rufe.

Obi ya yi magana ne yayin da yake mayar da martani kan rahoton yiwuwar haɗewar jam’iyyar Labour (LP) da PDP.

A wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na NoireTV-GlobalBlackTV da aka saki a YouTube a ranar Asabar, tsohon Gwamnan Jihar Anambra ya ce: “Ba na fatan zama Shugaban Ƙasa ido rufe, ina fatan ganin Nijeriya ta yi aiki, musamman ga talakawa.”

Dangane da batun goyon bayan Atiku ga takararsa idan za a yi haɗaka, tsohon ɗan takarar shugaban ƙasar na jam’iyyar LP ya ce: “Na yaba masa kuma ina godiya da kalamansa, musamman ma inda ya ce zai goyi bayana idan ya kasance (tikitin takarar shugaban ƙasa) ya tafi Kudu maso Gabas.

“Idan har haɗewar don a samu damar gudanar da mulkin Nijeriya yadda ya kamata ne, a buɗe dukkan abubuwan da za su sa Nijeriya ta zama wuri mai kyau, a shirye nake.”

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?