

Gabanin yajin aikin da ƙungiyar ƙwadago ta Najeriya ta shirya yi a faɗin ƙasar, wanda aka shirya gudanarwa a ranakun ashirin da bakwai da ashirin da takwas ga watan nan, Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya (NPF) ta ce ta sanya jami’anta cikin shirin ko-ta-kwana.
Rundunar ta kuma bayyana ƙudurinta na tabbatar da kare haƙƙin ‘yan ƙasa da ‘yancin yin zanga-zangar.
Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa a ranar Litinin, mai ɗauke da sa hannun Jami’in Hulɗa da Jama’a na Rundunar ta NPF, Olumuyiwa Adejobi.
“Rundunar ‘yan sandan Najeriya, a kan shirin gudanar da zanga-zangar da Ƙungiyar Ƙwadago ta Najeriya za ta yi, ta tabbatar da ‘yancin da ‘yan ƙasar ke da shi na gudanar da zanga-zangar lumana daidai da wasu dokoki. Don haka, NPF tana nanata ƙudurinta na tabbatar da kare haƙƙi da ‘yancin masu zanga-zangar.
“A bisa aikin da ya dace na tabbatar da doka da oda, rundunar ‘yan sandan Najeriya ta baza jami’anta a faɗin ƙasar tare da sanya su cikin shirin ko-ta-kwana domin sanya ido kan zanga-zangar da aka shirya. An sanar da dukkan Kwamishinonin ‘Yan Sanda da jami’an su na sa-ido tare da ba su umarni da su haɗa kan jami’an da ke ƙasa wajen tabbatar da tsaron dukkan mahalarta taron idan an gudanar da zanga-zangar kamar yadda aka tsara,”
NLC na nuna rashin amincewa da gazawar gwamnati wajen aiwatar da yarjejeniyoyin da ɓangarorin biyu suka cimma a ranar biyu ga watan Oktoban 2023, bayan cire tallafin man fetur.
Matakin dai ya biyo bayan kammala wa’adin kwanaki sha huɗu da aka ba gwamnatin tarayya na aiwatar da matakan yaƙi da wahalhalun da ke addabar ƙasar.
A cikin sanarwar, Adejobi ya ce duk da rundunar ‘yan sanda ta fahimci mahimmancin zanga-zangar, tana ci gaba da taka-tsan-tsan don hana duk wani yunƙuri na sace zanga-zangar, kuma jami’an za su daƙile duk wani yunƙuri na haifar da tarzoma, domin ‘yan sanda ba za su amince da karya doka da oda ba.
A cewar sanarwar, Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, Kayode Egbetokun, ya kuma yi kira ga masu zanga-zangar da su gudanar da ayyukansu cikin lumana da hankali tare da bin ƙa’idojin rashin tashin hankali da mutunta ‘yancin wasu, a yayin zanga-zangar.
“Duk da sanin muhimmancin zanga-zangar lumana, rundunar ‘yan sandan Najeriya na ci gaba da taka-tsan-tsan kan duk wani yunƙuri na sace zanga-zangar daga ɗaiɗaikun mutane ko gungun mutane masu mugun nufi. Saboda haka, rundunar ta shirya tsaf don mayar da martani cikin gaggawa ga duk wani aiki da ya saɓawa doka ko tashe-tashen hankula da ka iya yin barazana ga zaman lafiya da tsaron lafiyar jama’a, idan hakan ya faru,” in ji sanarwar.