Back

Zanga-zangar Yunwa, Tsadar Rayuwa An Toshe Hanyoyin A Minna

Daruruwan mazauna Minna, babban birnin jihar Neja, a ranar Litinin, sun gudanar da zanga-zangar nuna rashin amincewa da yunwa da tsadar rayuwa a kasar Najeriya, tare da toshe manyan tituna a cikin birnin.

An ji masu zanga-zangar da suka hada da mata da matasa suna rera wakokin zanga-zangar, yayin da jami’an tsaro ciki har da ‘yan sanda suka zura idanu domin kada abin ya wuce gona da iri..

Masu zanga-zangar sun ce tsadar kayan abinci da kuma rashin kokarin da gwamnati ke yi na kame lamarin ya tilasta musu rufe manyan tituna domin gwamnati ta ji kukan su.

Mataimakin gwamnan jihar Neja, Yakubu Garba, a lokacin da yake jawabi ga masu zanga-zangar, ya ce gwamnati na sane da kuncin rayuwa da iyalai ke fuskanta a wannan lokaci.

Ya ce gwamnati na kokarin rage tsadar rayuwa sakamakon cire tallafin man fetur

Wakilin Mu
Wakilin Mu
https://www.btvhausa.com

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?