Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya amince da naira biliyan ɗaya domin horar da malaman matakin farko a faɗin ƙananan hukumomi 27 na jihar.
Ya sanar da amincewar ne a ranar Talata a lokacin da yake ƙaddamar da sabbin sakatarorin ilimi na ƙananan hukumomi 27 da aka naɗa waɗanda za su gudanar da harkokin ilimin firamare a ƙananan hukumominsu.
Gwamnan ya bayyana cewa sama da malamai 1,000 da ke da takardar shaidar O-Level a matsayin mafi girman cancanta za su ƙara samun horon da zai ba su damar samun ƙarancin cancantar koyarwa.
Ya bayyana cewa horon zai shafi malaman da ba su da ilimin koyarwa amma aka gano cewa za a iya horar dasu bisa ga bayanan jarabawar cancanta da aka yi.
Zulum ya ƙara da cewa gwamnatin sa a shekarar 2019 da aka rantsar da shi, ta fara sake gina katafaren gine-ginen makarantu da suka lalace domin samar da ingantattun sakamakon koyo wanda a cewarsa hakan ya sanya adadin yaran da ba sa zuwa makaranta ya ragu zuwa dubu ɗari takwas daga cikin sama da miliyan biyu.
Gwamnan ya buƙaci sabbin sakatarorin ilimi da aka naɗa da su yi aiki yadda ya kamata sannan ya yi gargaɗin cewa za a maye gurbin duk wanda aka samu da gazawa.
“Dole ne in jaddada cewa tare da babban gata ne babban nauyi yake zuwa. Don haka na umurci Kwamishinan Ilimi da ya ba ni rahoton kwata-kwata kan ayyukan kowane sakataren ilimi. Za a maye gurbin waɗanda suka kasa cimma tsammani,” inji Zulum.