Back

Zulum ya naɗa mataimaka 168, mambobin hukuma 104

Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno

Gwamna Babagana Zulum na Borno ya amince da naɗin mataimaka 168 da mambobin hukuma 104 na hukumomi da kwamitocin jihar 15.

Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Sakataren Gwamnatin Jihar Borno (SSG), Alhaji Bukar Tijjani, ya fitar ranar Litinin a Maiduguri.

Ya ce waɗanda aka naɗa sun haɗa da Manyan Mataimakan Fasaha (STA) 9, Manyan Mataimaka na Musamman (SSAs) 81, da Mataimaka na Musamman (SAs) 78.

SSG ya kuma jero wasu 104 a matsayin shugabanni da mambobin hukuma na hukumomi da kwamitoci 15.

Hukumar ta SSG ta ce an yi naɗin ne bisa ikon da aka bai wa gwamnan ta hanyar tanadin Sashe na 208 (2) na Kundin Tsarin Mulkin Tarayyar Nijeriya na shekarar 1999 da aka yi wa gyara.

“Gwamnan na taya waɗanda aka naɗa murna tare da fatan bayar da gudunmawar da suke bayarwa wajen ci gaban Borno,” inji SSG.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?